1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tillabéri na fama da harin 'yan ta'adda

Gazali Abdou Tasawa LMJ
March 17, 2021

A Jamhuriyar Nijar gwamnatin kasar ta ayyana zaman makoki na kwanaki uku daga wannan Larabar, domin nuna alhini kan kisan wasu fararan hula kusan 60 da wasu 'yan ta'adda suka yi a yankin Banibangou na jihar Tillabéri.

https://p.dw.com/p/3qkUH
Niger Treffen der afrikanischen Union in Niamey - Mahamadou Issoufou
Shugaban Jamhuriyar Nijar mai barin gado Mahamadou IssoufouHoto: AFP/I Sanogo

Tuni dai kungiyoyin kare hakkin dan Adam a Jamhuriyar ta Nijar, suka fara tofa albarkacin bakinsu dangane da yadda matsalar tsaro ke kamari a yankin na Tillabéri duk da matakan tsaron da gwamnati ke cewa tana dauka. A cikin wata sanarwa da kakakin gwamnatin kasar Malam Zakariya Abdourahmane ya karanto a daren Talatar da ta gabata a gidan talabijin na kasa na Tele Sahel, ya ce maharan wadanda kawo yanzu ba a kai ga tantance su ba, sun tare wasu motoci hudu dauke da 'yan kasuwa da suka dawo daga cin kasuwar mako-mako ta garin Banibangouda kan hanyarsu ta koma wa garuruwansu na asali na Chinegodar da kuma Darey Dai.

Karin Bayani: Mummunan hari a Jamhuriyar Nijar

Toter Soldat in Mangaizé
Nijar ta jima tana fuskantar hare-haren ta'addanci musamman a yankin TillabériHoto: DW/M.Kanta

Kakakin gwamnatin ya kara da cewa, maharan sun sauko da su daga motoci tare da yi musu kisan dauki dai-dai bayan karbe musu dukiyoyi: "A kauyen Darai Dai maharan sun kashe mutane sun kuma kona rumbuna. A jumulce a cikin wadannan tagwayen hare-hare, mutane 58 sun halaka guda ya jikkata sun kuma kona runbunan abinci masu yawa da wasu motoci biyu kana sun yi awon gaba da wasu motocin biyu."

Yanzu haka dai mahukuntan na Nijar sun ayyana zaman makoki na tsawon kwanaki uku daga wannan Laraba a duk fadin kasar. Sai dai Tuni dai kungiyoyin kare hakkin dan Adam na kasar ta Nijar irin su Alternative Espace citoyen ta bakin shugabanta Malam Moussa suka soma nuna damuwarsu da halin da ake ciki a Jihar ta Tillabery duk da matakn sojan da ake dauka a yankin.

Karin Bayani: Harin ta'addanci a barikin sojojin Nijar

Ita ma dai kungiyar MPCR ta Malam Nouhou Arzika ta bakin daya daga cikin shugabanninta Malam Nayoussa Jimraou a martaninta cewa ta yi, lokaci ya yi da ya kamata a zaunar da rukunnan kabilun jihar ta Tillabéri kan tebur domin gano bakin zaren warware matsalar. Gwamnatin ta Nijar dai ta sanar da aikawa da karin sojoji a yankin da kuma tsaurara matakan tsaro domin farauta mutanen da suka aikata wannan aika-aika da nufin kamo su a kuma gurfanar da su a gaban kuliya.