Nijar za ta yaƙi Boko Haram | Labarai | DW | 06.02.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Nijar za ta yaƙi Boko Haram

Rahotanni daga birnin Yamai na jamhuriyar Nijar, na cewar gwamnatin Nijar ta shirya tura dakarunta zuwa Najeriya don yaƙar Boko Haram.

Matakin da ke zuwa a dai dai lokacin da mayaƙan Boko Haram ke kashe-kashe a kan iyakokin Najeriyar da makwabtan nata, mahukuntan na Nijar na ganin zai buɗe kafar tinkarar ƙungiyar gaba-gadi daga arewaci.

Boko Haram dai ta kashe sama da mutane ɗari a Larabar da ta gabata, ciki har da soji 19, a wani harin da ta ƙaddamar a garin Fotokol da ke iyaka da Najeriya.

Mawallafi Muntaqa Ahiwa
Edita Abdourahamane Hassane