Nijar: ′Yan adawa sun yi babbar zanga-zanga | Labarai | DW | 11.11.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Nijar: 'Yan adawa sun yi babbar zanga-zanga

A wannan Lahadin ne dubban jama'a suka fito a birnin Yamai domin amsa kiran 'yan dawa wajen nuna adawarsu da kundin zaben kasar ta Nijar da suke zargin bangaran gwamnati da shirya manakisa a game da zaben.

Tsohon shugaban kasar ta Jamhuriyar Nijar Alhaji Mahamane Ousmane ne dai ya jagorancin wannan zanga-zanga wadda wasu ke fadin ba'a taba ganin irinta ba daga cikin jerin zanga-zangar da 'yan adawan ke shiryawa a birnin na Yamai. Wani kudiri ne dai mai lamba takwas na kundin zaben kasar ta Jamhuriyar Nijar ke kan gaba wajen haddasa cecekuce a kasar. Wannan kudiri kuma ka iya haramta wa madugun 'yan adawan kasar Hama Amadou tsayawa takara a zabukan kasar masu zuwa abin da 'yan adawar na Nijar suka ce ba za ta sabu ba.