Nijar: ′Yan adawa na son Bazoum ya sauka | Siyasa | DW | 04.04.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Nijar: 'Yan adawa na son Bazoum ya sauka

A cikin wata sanarwa da suka bayyana hadin gwiwar jam'iyyun siyasa na adawa sun nemi da shugaban Kasar Nijar Mahamadou Issoufou ya sauke Mohamed Bazoum daga matsayin ministan cikin gida.

Mohamed Bazoum ministan cikin gida na Nijar kuma shugaban jam'iyyar da ke yin mulki PNDS Tarraya

Mohamed Bazoum ministan cikin gida na Nijar kuma shugaban jam'iyyar da ke yin mulki PNDS Tarraya

Sanarwar mai dauke da sa hannun shugaban hadin gwiwar jam'iyyun siyasar na adawa na FRDDR, an yi ta ne da sunan ‘yan adawar kasar ta Nijar baki daya, inda suke neman da a sauke Mohamed Bazoum daga mukaminsa na ministan cikin gida bayan da aka nadashi dan takarar neman shugabancin kasa. 'Yan adawar sun ce ba daidai ba ne Bazoum din ya ci gaba da rike matsayin minista cikin gida bayan jam'iyyarsa ta bayyana takararsa a zaben shugaban kasa na shekara ta 2021.

Sauti da bidiyo akan labarin