1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kawata biranen Nijar saboda bikin jamhuriya

Salissou Boukari AH
December 18, 2019

Bukukwan gudanar da cikon shekaru 61 da Nijar ta zama jamhuriya cikin juyayi na rashin sojoji 71 da kasar ta yi a sakamakon hare-hare na kungiyar IS da ta kai a barakin sojin Inates.

https://p.dw.com/p/3V0xK
Demokratische Republik Kongo Kinshasa | Nigerianischer Präsidenten Mahamadou Issoufou
Hoto: Presidence RDC/G. Kusema

A Jamhuriyar Nijar an kammala faraitin sojoji a birnin Tillabery da ke yammacin kasar albarkacin zagayowar cikon shekaru 61 da kasar ta zama Jamhuriya. Kuma a kowace shekara ana zaben wata jiha inda ake kawatata, tare da aiwatar da gine-gine ta yadda za ta karbi bakuncin manyan mutane har' ma shugabannin kasashe. A wannan karo shagulgullan na birnin Tillabery sun samu halartar shugabannin kasashen Ghana da na Burkina Fasso. Tun dai daga lokacin Diori Hamani, zuwa shugaban kasa na mulkin soja Seyni Kountche ne aka soma irin wannan tsari na raya birane, inda a wancan lokaci aka yi gine-gine da dama da har yanzu ake cin moriyarsu.

Kawata biranen Nijar saboda bikin jamhuriya ya yi tasiri wajen gina biranen Nijar

Niamey Nigeria
Hoto: Getty Images/AFP/B. Hama

Issoufou Tamboura dan siyasa ne da ya san yadda wannan lamari ya tabo takaitaccen tarihin wannan biki da ya ce yake ba da damar samar da gine-gine a cikin birane. Wannan biki dai na ran 18 ga watan Disamba na tunawa da Nijar ta zama jamhuriya ya kasance wata babbar dama da cudanya tsakanin al’umma na jihohi dabam-dabam kuma gine-ginen da ake yi na raya birane duk da yake ma ana samun kura-kurai masu yawa. A shekara mai zuwa dai wannan biki za a yi shi ne a birnin Diffa, wanda yake fama da matsaloli na tsaro na rikicin Boko haram, kuma ana ganin wannan wata dama ce da za a kawo babban gyara ga birnin na Diffa tare da inganta wurare da dama da suka lalace. Ana dai gudanar da wannan biki ne cikin juyayi na rashin sojoji 71 da kasar ta yi a sakamakon hare-hare na kungiyar IS da ta kai a barakin soji na  Inates.