1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar taƙaddama gabanin zaɓen ƙasar

Abdoulaye Mamane Amadou/AHJanuary 29, 2016

Jam'iyyun adawar sun kai gwamnatin ƙara a gaban kotu cewar hukumomin na yin amfanin da sarakunan gargajiya saboda zaɓen ƙasar.

https://p.dw.com/p/1Hlt6
Niger Präsident Mahamadou Issoufou
Hoto: F. Batiche/AFP/Getty Images

'Yan adawar sun ce dokokin tsarin mulki na ƙasar sun haramta wa sarakunan gargajiya shiga duk wani lamari na siyasa. To amma duk da hakan sarakunan na cikin harkokin siyasar ƙasar

Shigar sarakunan gargajiyar a cikin harkokin siyasa

Hon Abdoul Kadri Tidjani ke nan sakataren jam'iyyar MNSD NASARA mai adawa kuma kakakin ƙawancen jam'iyyun adawar ƙasar ke tabbatar da shigar da ƙarar majalisar sarakunan bisa zarginsu da taka rawa a cikin harkokin siyarsa domin goyon byan gwamnatin.

Seini Oumarou Vorsitzender der Partei MNSD im Niger Afrika
Hoto: MNSD


Kalamun na Tidjani Abdoul Kadri na zuwa ne 'yan kwanaki ƙalilan bayan aikewa da wata wasika da madugun 'yan adawar ya yi wa majalisar ta sarakunan gargajiya a tsakiyar wannan wata yana mai yi wa majalisar dama sarakuna da su guji yin shishigi ko nuna fifiko tsakanin wane da wane a fagen siyasa. Ganin irin rawa da ma matsayin da sarakunan suke da shi a bainar jama'a sai dai duk da hakan 'yan adawar sun ce sarakunan na ci gaba da aikata abin da 'yan adawar suka kira laifi ga dokokin tsarin mulki.

Shaidu na hanun sarakunan a cikin yaƙin neman zaɓe

'Yan adawar sun ce su ganau ne a kan wannan batu da gwamnati ke ɗauka a matsayin zargi,inda suka tabbatar cewar da anyi mahawara misali a jihar Maradi inda gwamna ya kira sarakunan gargajiya ya kuma umarcesu da su yi wa shugaban ƙasa mai ci yanzu, yaƙin neman zaɓe.Hon,Tidjani Abdoul kadri ya ce nan gaba idan har shari'a ta fara aikinta to duk wanni basaraken ko baruman da aka kama da aikata wannan laifin ya kuka da kansa.

Niger Strassenszene Markt
Hoto: AP