Nijar: Shekaru 25 bayan taron kasa | Siyasa | DW | 29.07.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Nijar: Shekaru 25 bayan taron kasa

Wadanda suka yi ruwa da tsaki wajan kaddamar da taron na shekaru 25 baya, na masu ganin halin da a ke ciki a yau a fagen siyasar Nijar sun kauce wa tsari.

Niger Präsident Mahamadou Issoufou

Shugaba Mahamadou Issoufou

A Jamhuriyar Nijar a yayin da hankali ya karkata ga bukukuwan karrama ranar zagayowar shekaru 25 da gudanar da wani babban taron kasar (Conférence Nationale) da ke a matsayin matattakalar turbar dimokuradiyya a kasar bangarori daban-daban ne cikinsu har da wadanda suka halarci taron ke bitar tsarin da kasar ta bi tun daga lokacin zuwa yau da wasu raayoyi mabanbanta. A yayin da wasu ke ganin an samu ci gaba a fanoni daban-daban wasunsu kuwa cewa suke 'yan siyasar kasar ba su yi adalci ba ga babban taron.


Tun a matakin farko dai makasudin kiran taron na da nufi ne na share mulkin da ake kallo irin na danniya da kama karya wanda ya tauye 'yancin zartar da dimokuradiyya face na jamiyya tilo da ke makale da 'yancin fadar albarkacin baki da danne yaduwar kungiyoyin da suka shafi farar hula da na 'yan kwadago, duk ko da bukatar hakan da ke da akwai a lokacin sakamakon sauyawar alamura.

Niger Niamey Opposition

Fafutika da adawa a Nijar ba bakón abu ba ne

Tsawon watanni uku dai mahalarta taron daga rassa daban-daban na kasar sun samar da wata taswira da ake kallo tamkar ita ce matattakalar yaduwar kungiyoyi na siyasa da bayyanar kafafen yada labaru uwa uba batun dorewar dimokuradiyya ta hanyar jamiyyu barkatai.

Sai dai tuni wadanda suka yi ruwa da tsaki wajan kaddamar da taron na shekaru 25 baya, na masu ganin halin da a ke ciki a yau a fagen siyasar Nijar sun kauce irin tsari da manufofin da taron ya shata.

Malam Mohamed Moussa na daya daga cikin shika-shikan taron:

Moussa Tchangari, Journalist und Menschenrechtler

Moussa Tchangari wakilin dalibai a taron kasa shekaru 25 da suka wuce

"Manufofin babban taron tun yaushe an mance da su domin akwai kura-kurai saboda wanda ya samu iko sai ka ga na amfani da karfi har yanzu, baa bin hanyoyin gaskiya. Sai dai duk da haka mun fi kasashe da yawa."

Shekaru 25 na bayan taron, masu sharhin na ganin tamkar kauce wa tsari ne da kaidojin da taron ya rataya a wuyan gwamnatoci na yau inji Moussa Tchangari, jagoran dalibban Nijar da suka halarci taron na Conférence nationale

"Duk wadanda suka zo har zuwa yau ai yawanci jama
a suka zabe su, kuma jamaa ba su zabi kowa don a yi masu rashin adalci ba, kenan wadanda aka ba wannan amanar su suka ci amana, yawanci su suka ci amanar mutane kuma zaa iya a duba nan da shekaru 25 baya, wane ya yi laifi, wace gwamnati ta aikata ba dai dai ba, ko wane shugaba ana iya gani kuma mutane su fadi idan ya yi abin alheri kenan mutane na ganewa ga wadanda suka ci amanar 'yan kasa."

Sauti da bidiyo akan labarin