Nijar: Sarrafa kayan shafe-shafe da Itatuwa | Himma dai Matasa | DW | 22.11.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Himma dai Matasa

Nijar: Sarrafa kayan shafe-shafe da Itatuwa

A Jamhuriyar Nijar wata matashiyar ta rungumi sarrafa diyan itace na bedi (dogon yaro) da aduwa don yin sabulun wanka da wanki da mai na shafawa mai gyara jikin jama'a.

Masu cin gajiyar wannan kayan dai su ne mata da yara da ma masu karamin karfi. Sai dai duk da wannan yunkurin matashiyar ta koka da rashin tallafi na gwamnati da ma rashin sayen kayan da ta ke sarrafawa daga jama'a abubuwan da ke iya kawo cikas ga kwazon matashiyar da fasahar da ta samar da ke da niyar inganta lafiyar jama'a musamman mata da yara-Wakilinmu daga Yamai Abdoulaye Mamane Amadou ya duba muna wannan batun ga kuma Rahotonsa 

Matashiyar kan yi amfani ne da diyan itace na dalbejiya ko dogon yaro da na ba wa da diyan aduwa don jujjuyasu izuwa ga ababen amfani da more rayuwar jama’a a wani yunkurin da ta ke da shi na kawo dauki da agaji da ma tallafawa masu karamin karfi, musamman mata da kananan yara a wannan lokaci na sanyi.

Duk da yake Nijar na daga jerin kasashen Sahel masu fama da Hamada da Sahara Allah ya albarkaci Jamhuriyar ta Nijar da tarin Aduwa da Dalbejiya. Sai dai wasu lokutan jama’a na banza da irinn albarkatun da ke tattare da diyan itacen mai makon saka tsari da sarrafasu, sai kuma jama’a su rinka hangen wasu kayayakin da ake shigowa da su daga nesa alhali kuwa a yanzu Allah ya kawo nesar a kusa duba da tarin matsalolin rayuwa da matsin tattalin arziki da ke samun gindin zama ga jama’a.