Nijar: Sabon hukunci kan cikin jarirai | Siyasa | DW | 01.06.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Nijar: Sabon hukunci kan cikin jarirai

Wata sabuwar bakala mai nasaba da cinikin jarirai a Nijar ta dauki wani salo bayan sake daure wasu manya sama da mutum 20.

Cece-kuce ya kunno kai ne bayan zartar da hukuncin kotu kan shari'ar da aka yi wa mutanen da aka same su da laifin cinikin jarirai kimanin mutane 23 ma'aurata maza da mata daga ciki har da uwargidan tsohon kakakin majalisar dokoki kuma jagoran adawa Madam Hama Hajiya Hadiza Amadou, da tsohon ministan noma Alhaji Abdou Labo.

An dai kai su gidajen kaso na garin Say da kuma Kollo bayan shari'ar da aka yanke masu yi musu inda za su yi zaman shekara daya, bayan shafe watanni shida a tsare gidajen kason kafin alkali ya gama bincike yai musu sakin talala. A yanzu zasu yi zaman watanni shida cikamakon shekara daya kenan da kotun ta yanke musu hukunci.

Shugabannin kungiyoyin farar hula dai sun ce dai dai ne kotu ta rika yin shari'a amma sun zargi hukumomi da yi wa alkalan katsalandan. A cewar alhaji Salisu Amadu mamba a kungiyar rajin kare hakin dan adam, ba suna kare wani ko wasu ba ne, su na kokowa ne a yi aiki da doka.

Duk wanda ya aikata makamancin wannan laifin ya kyautu ya gurfana gaba kuliya, amma ba haka abin yake ba; domin kwanan nan wasu sun yi laifi bayan kamasu daga baya kuma aka sake su.

Sai dai abin da mutane ke tambaya a nan shi ne, kotu bata bayyana makomar yaran da aka sayo su ba. Nan ma Salisu cewa ya yi.

''Mene ne matsayinsu, za'a kai su kaso ne su ma kogi dan renon marayu  za'a kai su, ko kuwa za a mayar da su Najeriya inda aka sayo su?

Su ko a nasu bangaren 'yan siyasa na adawa sun ce ba komai ba ne illa bita da kulli ne mahukunta suke yi musu, kamar yadda Alasan Incinikar mataimakin kakakin hadin gwiwar jam'iyyun adawa cewa ya yi.

''Jagoran adawa Hama Amadou, hukumomi sun nemi lafin da za su dora masa basu samu ba shi ya sa suka bullo da wannan kagen cinikin jarirrai. Abin da yake nuna cewa kokari ne hukumomi ke yi na neman murkushe adawa''

Sai dai shi Hama Amadou, bayan shari'ar da kotunan Nijar suka yi kan wannan badakalar cinikin jarirai, ya garzaya kotun kungiyar gamayyar tattalin arzikin kasashen afrika ta yamma CEDEAO inda ya shigar da kara, wanda ake jiran hukuncin da zata yanke a kai.