1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar: Sabbin matakan yaki da cin hanci

Abdoulaye Mamane Amadou UAA
January 10, 2018

Kungiyoyin yaki da cin hanci da rashawa a Nijar sun nuna shakku game da sabbin matakan da gwamnati ta ce ta dauka na sanya kafar wando guda da masu aikata laifin cin hanci da rashawa.

https://p.dw.com/p/2qeIE
Niger Präsident Mahamadou Issoufou
Hoto: F. Batiche/AFP/Getty Images

Duk da matakan da gwamnatin Nijar ke dauka dangane da batun na cin hanci da rashawa tsawon shekaru, hukumomin kasar sun ce har yanzu akwai sauran rina a kaba inda matsalolin cin hanci da rashawa ke kara kamari tare da illata daukacin fannonin kasar da kawo tarnaki wajen bunkasar tattalin arzikinta.

Wadannan dalilai suka kai ga gwamnati samar da wani sabin kundin wanda babban burinsa shi ne na yin ba sani ba sabo ga duk wadanda ake tuhuma da rub da ciki ko barnata dukiyar kasa.

Gwamnatin kasar ta rattaba hannu ga sabon kundin a yayin wani zaman taro na majalisar ministoci da zummar bai wa hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta kasar wato HALCIA damar shigar da karar duk wani dan kasar da take zargi ko ta ji labari da aikata laifi, ko da kuwa a ginin gidaje ne bayan ta gudanar da bincike a sassa dabam-dabam kana kuma ba tare ma da tuntubar fadar shugaban kasa ba don samun umarni sabanin yadda take aikinta a baya.

Tababa kan sabon kundi yaki da cin hanci

Hukumar HALCIA na wayar da kai don kawar da karbar na goro
Hukumar HALCIA na wayar da kai don kawar da karbar na goro

Ba tun yau ba manazarta al'amuran yau da kullum ke yi wa batun na cin hanci da rashawa a Nijar kallon zancen 'yan matan amarya duba da kwan gaba kwan bayan da ake yi idan har an hadu da wasu shafaffu da mai ko masu karfin mukami a cikin mulkin kasar, lamarin  da a yanzu shugaban hukumar ta HALCIA Gousmane Abdourahmane ya ce duk masu irin wannan aiki su kuka da kansu.

Sai dai har gobe wasu kungiyoyin kare hakin jama'a na kasancewa a cikin shakku duba da yadda aka jima ana hattara sa ba tare da sun ga kaho ba.

Yanzu haka dai hukumar ta cafke wasu masu fada a ji da ke rike da mukamai a wani sashe na ma'aikatar albarkatun noma. Yanzu haka hukumar na gudanar da bincike a hukumar alhazzai ta COHO da kuma wani fanni na ma'aikatar man fetur inda ake zargin aikata masha'a da dukiyar al'umma.