Nijar: Riga malam masallaci na ′yan siyasa | Siyasa | DW | 25.03.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Nijar: Riga malam masallaci na 'yan siyasa

Manyan jam'iyyun siyasa a Nijar na ci gaba da bayyana 'yan takararsu a zaben shugaban kasar na 2021, abin da ke janyo cecekuce.

A Jamhuriyar Nijar manya-manyan jam'iyyun siyasar kasar na ci gaba da bayyana 'yan takararsu a zaben shugaban kasar da zai gudana a shekarar 2021, abin da ke ci gaba da janyo cecekuce a tsakanin masharhanta da ke ganin wannan wani sabon salo ne da 'yan siyasa suka fito da shi na nuna gaggawa cikin lamuransu.

Ganin yadda wannan lamari na siyasar kasar ta Nijar ya yi kamari, ya sanya tsohon shugaban hukumar koli ta sadarwa ta kasa ya yi wani rubutu ta shafinsa na Facebook, inda ya ke tunatar da 'yan siyasa na kasar cewa dokokin da kundin zaben kasar ya tanada sun bayyana karara yadda ta kamata 'yan siyasa su gudanar da shagulgulansu a siyasa cikin tsari na doka.

Ga misali kuduri mai lamba 91 na kundin zaben kasar ta Nijar na 2017 na cewa kafin a buda yakin neman zabe, duk wata farfaganda ta neman magoya baya a bayyane ko a fakaice, ko duk wata sanarwa a bainar jama'a ta nuna goyon bayan wani dan takara, ko wata jam'iyya da hadin gwiwar jam'iyyun siyasa ya haramta ga kowa. Nauyi ne kuma ya rataya ga hukumar sadarwa ta kasa da ta sa a yi biyayya ga wannan hani na doka.

Nouhou Arzika mai fafatuka na farar hula a Nijar

Nouhou Arzika mai fafatuka na farar hula a Nijar

Baya ma ga masharhanta da ke bibiyar yadda harkokin siyasa kasar ta Nijar ke gudana, su ma daga nasu bangare kungiyoyin fararan hula ta bakin Malam Nouhou Arzika shugaban hadin gwiwar kungiyoyin da ke fafatukar kare hakin jama'a da neman ganin an yi gaskiya cikin tafiyar da harkokin mulki a Nijar sun soki lamirin wannan mataki na 'yan siyasa ta Nijar.

Da dama dai daga cikin 'yan kasar na ci gaba da yi wa wannan mataki na 'yan siyasar na riga malam masallaci fahimta ta dabam, inda kowa ke tofa na shi albarkacin baki kan dalillan da yake ganin suka kawo hakan.

Abin jira a gani shi ne na matakin da hukumar zabe da kuma hukumar sadarwa ta kasa za su dauka wajen takawa 'yan siyasa birki don ganin sun mutunta dokokin kundin zaben kasar.

Sauti da bidiyo akan labarin