1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Cin-hanci

Yaki da cin-hanci da rashawa a Nijar

Salissou Boukari LMJ
December 9, 2021

Hukumar Yaki da Almundahana da Kudin Al'umma ta Jamhuriyar ta Nijar wato HALCIA, ta shiya wani kasaitaccen bikin ranar yaki da cin-hanci da rashawa ta duniya.

https://p.dw.com/p/443ph
Deutschland l Besuch des Nigerianischen Präsidenten in Berlin
Yaki da cin-hanci a Nijar, na daga cikin kalubalen gwamnatin Mohamed BazoumHoto: Presse- und Kommunikationsdienst der Präsidentschaft von Niger

Da yake jawabi yayin bikin na bana, shugaban hukumar ta HALCIA mai shari'a Mai Moussa Alh Bassir ya ce taken ranar ta bana wato: "'Yancinku abin da ya kamata ku yi kuce baku yarda da cin-hanci ba", na kira ga kowa daga inda yake domin ya nisanci akidar cin hanci.

Karin Bayani: Bankado badakalar cin-hanci a harkar mai a Nijar

Da yake tofa albarkacin bakinsa kan wannan batu Honorable Alio Namata mamba a kungiyar 'yan majalisar dokoki na kasa masu yaki da cin hanci, ya ce sai fa kowa ya tashi tsaye idan ana so a magance matsalar cin hanci. Babbar ayar tambayar da al'umma ke azawa ita ce, wai shin ina batun mutanen da suka rike manyan mukamai da aka zarge su da laifin karkata akalar kudin kasa. Shin mai HALCIA ta yi kan irin wadannan mutane? 

Niger | Ouhoumoudou Mahamadou
Firaministan Jamhuriyar Nijar Ouhoumoudou MahamadouHoto: PNDS Tarayya Partei

A nasa jawabin firaministan Jamhuriyar ta Nijar Ouhoumoudou Mahamadou ya ce kirkiro hukuma ta yaki da cin hanci kadai da aka yi, babban mataki ne na yakar cin-hanci wanda kuma a yanzu gwamnati ke bayar da cikakken goyon baya: "Shugaban kasa da kanshi ya samu ganawa da dukannin masu ruwa da tsaki a fannin yaki da cin-hanci da karbar rashawa, kuma ya ba su cikakken umarni kan wannan matsala ta cin-hanci. Wannan babban mataki da shugaban kasa ya dauka ya ba mu damar saka tsare-tsare na yaki da cin hanci a cikin kundin gudanarwa na aikin gwamnati, inda za mu kara bayar da karfi wajen bita da karfafa matakan yaki da cin-hanci."

Karin Bayani: Yaki da cin-hanci tsakanin malaman Nijar

A nasa bangaren Alhaji Idi Ango Omar tsohon ministan cikin gida na Jamhuriyar Nijar kuma mamba a kungiyar tsofaffin manyan ma'aikatan gwamnati CIRAC masu kishin ganin an yi aiki da dokokin kasa cewa ya yi, idan da za a sakarwa HALCIA da alkalan shari'a mara to da cin-hanci ya kare.