Nijar na neman daidaita sahun kungiyoyi | Siyasa | DW | 29.05.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Nijar na neman daidaita sahun kungiyoyi

Ministan cikin gidan NIjar ya bai wa kungiyoyin farar hula wa'adin yni rijista, idan ba sa son fuskantar fushin hukuma, batun da kungiyoyin suka ce sun gane ko mai yake nufi.

Ministan cikin gida ne ke da nauyin tafiyar da harakokin kungiyoyi a Nijar. Saboda haka ne ya umarci kungiyoyin fara hular da ba su zabura don yin rejista har zuwa ranar 29 ga watan Mayu ko kuma su hadu da fushin gwamnati. Doka ta tanadi daurin wata daya zuwa shekara daya a gidan kaso, da kuma tara ta daga jikka 10 zuwa jikka 200 na CFA ga shugabannin kungiyoyin da ba su yi rejista ba.

Ra'ayoyi mabanbanta a kan matakin

Sai dai tuni wanann mataki ya soma haifar da muhawara a kasar ta Nijar. Nouhou Arzika shugaban kawancen kungiyoyin farar hula na MPCR na ganin matakin ya sabawa kundin tsarin mulkin kasar. Wasu daga cikin kungiyoyin farar hula na ganin cewa matakin ba shi da wata illa idan dai ba wata boyeyyiyar manufa ba ce gwamnatin ke da ita ba, a cewar Nassirou Seidu na kungiyar Muryar talakka.Wannan mataki ya zo ne daidai lokacin da wasu kungiyoyin farar hula kimanin 50 na Nija su ka hade a karkashin wani kawance daya da su ka yi wa lakabin da kawancan ceto Nijar wato "sauvons le Niger", wanda kuma ya soma kalubalantar wasu daga cikin manufofin gwamnatin kasar. Malam Nouhou Arzika daya daga cikin shugabannnin wanann sabon kawance na ganin ministan ya dauki matakin ne a wani yinkuri na taka masu birki.

Sai dai kokarin da na yi na jin ta bakin ofishin ministan cikin gidan dangane da wannan batu ya ci tura.

Mawallafi: Gazali Abdou Tasawa
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe

Sauti da bidiyo akan labarin