Nijar na cikin ruɗanin siyasa | Siyasa | DW | 20.11.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Nijar na cikin ruɗanin siyasa

Ana ci-gaba da faɗi na faɗa tsakanin jam'iyyun siyasa a Jamhuriyar Nijar, inda ɓangarorin ke ci-gaba da sukar juna

A jamhuriyar Nijar ƙawancan jam'iyyun da ke yin mulki na MRN ya fitar
da sanarwa. Inda ya mayar da martani a kan jerin wasu zarge-zarge da ƙawancan jam'iyyun adawa na ARDR ya yi wa shugaban ƙasar ta Nijar da gwamnatinsa a cikin wata sanarwa da su ka fitar a makon da ya gabata. Haka zalika ƙawancen jam'iyyun da ke milkin ya bayyan gamsuwarsa da rinjayen da ya samu a mahawarar gwada farin jinin gwamnati da aka gudanar a majalisar dokokin ƙasar a cikin watan jiya


Wahlen im Niger. Kandidat Hama Amadou. Personen; Politik; Bundestagswahl; Wahlen; Niger; Präsidentschaftswahlen; Wahllokal; Afrika; Politiker; Präsidentschaftskandidat; Wahl; persons; politics; election; politicians; political; vote; B950_168021; B950; elections; contest; general; politician; poll;

Jagoran Lumana, Hama Amadou

Ɗaya daga cikin batutuwan da ƙawancen jam'iyyun da ke mulkin ƙasar ta
Nijar na MRN ya mayar da martani a kansa a cikin sanarwa ta sa, shi ne na
zargin sakaci da 'yan adawar su ka ce gwamnatin ta yi dangane da
haɗarin mutuwar yan Nijar 92 a cikin sahara yau da yan makonni. Dokta
Sagir shugaban jam'iyyar PDP Bushara, shi ne Kakakin wanann sanarwa ta ƙawancan jam'iyyun da ke mulkin na MRN.

Archivbild vom 6. Dezember 19965 zeigt den Präsidenten von Niger, Mahamane Ousmane, bei einem Besuch der Elfenbeinküste. Das Militär in dem westafrikanischen Staat hat den Präsidenten am Samstag durch einen Putsch gestürzt. Der entmachtete Ousmane war im April 1993 als erstes Staatsoberhaupt Nigers demokratisch gewählt worden.

Mahamane Ousmane Shugaban CDS.Haka zalika a cikin sanarwar da ƙawancen jam'iyyun adawar na ARDR ya yi
a baya, ya zargi shugaban ƙasar da nuna ƙabilanci dama ɓangaranci a
cikin tafiyar da mulkinsa. Suna masu ba da misali da wani karin magana
na ɗan ƙaramin gatarinka ya fi sari ka bani. Su ka ce shugaban ƙasar
ya ce lokacin wani taro da ya gudanar a cikin jiharsa ta aihuwa ta
Tawa. Dangane da wanannan zargin da jam'iyyun masu mulki na MRN
ya mayar da martani yana mai cewa.

Presidential candidate Seini Oumarou, a former prime minister under deposed president Mamadou Tandja, casts his vote in Niamey, Niger, Monday, Jan. 31, 2011. This impoverished country on the edge of the Sahara took another stab at democracy Monday when it voted for a new president and parliament that are expected to take over leadership from the military.(Foto:Tagaza Djibo/AP/dapd)

Seini Oumarou, jagoran MNSDDaga ƙarshe dai ƙawancan jam'iyyun da ke mulkin ya sake jaddada goyon
bayansa ga shugaban ƙasa da gwamnati sa tare da sake sanya kira ga 'yan adawa masu ra'ayin kishin ƙasa, da su zo su kawo wa gwamnatin goyon bayansu domin gina ƙasa

Mawallafi: Gazali Abdou Tasawa
Edita: Usman Shehu Usman

Sauti da bidiyo akan labarin