1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar: Mutane miliyan 3 na bukatar agaji

Binta Aliyu Zurmi
February 19, 2020

MDD ta ce mutum kimanin miliyan uku na bukatar agaji cikin gagawa a jamuriyar Nijar, rabinsu mata ne da yara kanana da ke cikin matsanancin halin rayuwa a sakamakon iftala'i ko kuma wadanda rikicin tsaro ya rutsa da su.

https://p.dw.com/p/3Y1Bd
Afrika - humanitäre Hilfe im Tschadsee-Gebiet
Hoto: picture-alliance/AP Photo/A. Harnik

A wani rahoton Asusun kula da yara ta Majalisar wato Unicef ta bakin Felicite Tchibindat, wakiliyar Unicef a yankin ta ce, jama'a na cikin yanayi na bukatar taimako a yayin da suke fuskantar barazanar tsaro daga masu tayar da kayar baya. Amma sun rungumi kaddara duk da matsin da suke ciki inji wakiliyar wanda ta ce abin koyi ne ga sauran kasashen duniya.

Sanarwar na zuwa ne bayan wani iftala'i a ranar Litinin din da ta gabata, inda mata da yara akalla 20 suka mutu a sakamakon wani turmutsitsi a wani sansani da ake rabon abinci da kudi wa 'yan gudun hijira.