1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar: Muhawara kan sojin kasashen ketare

Abdullahi Tanko Bala
April 22, 2022

'Yan majalisar dokokin jamhuriyar Niger sun fara muhawara kan daftarin kudiri da nufin amincewa don tsugunar da rundunar musmaman ta sojojin tarayyar Turai da ke yaki da yan tada kayar baya a yankin Sahel.

https://p.dw.com/p/4AJVW
Nijar Niamey | Majalisar dokoki
Hoto: Gazali A. Tassawa/DW

Shugaban kasar Bazoum Mohammed a watan Fabrairu ya amince da karbar sojojin Faransa da za su baro kasar Mali.

Sojojin na Faransa kimanin 2,400 tare da sojojin musamman su 900 da ke cikin rundunar Takuba da Faransa ke jagoranta ake sa ran za su baro Mali cikin 'yan watanni masu zuwa sakamakon tabarbarewar dangantaka da sojojin da ke mulki a Malin.

Ana dai fargabar cewa janyewar sojojin ka iya haifar da karuwar tarzomar 'yan al Ka'ida da na kungiyar IS da suka yi sanadiyar mutuwar daruruwan mutane da kuma tagaiyara miliyoyin jama'a a yankin Sahel.

Bazoum ya mika daftarin kudirin ga majalisar dokoki domin sahalewa sojojin Faransa da na tarayyar Turai su zauna a Nijar don taimaka wa yaki da 'yan ta'adda wanda hakan zai taimaka wajen kare kasashen Nijar da kasashen gabar kogi da suka hada da Jamhuriyar Benin da Ghana da kuma Ivory Coast.