Nijar: Matsafa da al′adun gargajiya | Zamantakewa | DW | 07.07.2020
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Nijar: Matsafa da al'adun gargajiya

A Jamhuriyar Nijar har yanzu matsafa magadan gargajiya na rike da wata al'adar da ake kira ''Tarkama'' da ke tattare da mamaki da ke zakulo masu aikata barna daga cikin al'umma, batun da shirin Taba Ka Lashe ya duba.

Wannan wani tsohon hoto ne muka yi amfani da shi

Wannan wani tsohon hoto ne muka yi amfani da shi

Duk da shigowar addinin Musulunci har yanzu magada al'adu na shirya a wasu sassan Nijar irin su Tahoua abubuwa na gargajiya na a'aldu. Daya daga cikin dadaddun gargajiya da ake ci gaba da raya su ita ce al'adar Tarkama da ake shiryawa a duk lokacin da wasu ko wani daga cikin al'umma ya aikata wani laifi kamar na maita. Tarkama ke nuna mai laifin a cikin bainar jama'a duk inda ya boye. Matsafi Shaibu shi ne shugaban matsafa na garin Dagarka da ke Konni na Jihar Tahoua, ya ce al'adar na yin tasiri a kan rayuwar al'umma ta yau da gobe. Kamar sauran sabgogi wannan sabgar ta Tarkama dai ba ta yiwuwa sai dai matasa majiya karfi wadanda ake amfani da su wajen tada Takarmar. Dubban mutane ne dai ke zuwa kallon al'adar a duk lokacin da ake yin ta.