Nijar: Matashiya mai aikin buga katunan aure | Himma dai Matasa | DW | 20.11.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Himma dai Matasa

Nijar: Matashiya mai aikin buga katunan aure

Wata matashiyar da ta kammala karatunta ba ta samu aiki ba a Nijar, ta bude wani kamfani da ke yin aikin buga katunan aure ko suna da kuma buga riguna na tshirt.

Matashiyar dai Salamatou Boubacar mai shekaru 33 da haifuwa ta yi karatunta ne a jami'a inda ta karanci fanin lisafi. Sai dai ganin cewar ba ta samu aiki ba na gwamnatin hakan ya sa ta yi tunanin kirkiro nata kamfanin, wanda ya kunshi ma'aikata da dama da ke a karkashinta suna aiki. Kamfanin yana aikin buga katunan aure ko suna da kuma riguna wanda takan sayar da su a bisa kasuwanni. Babban tallafi da kamfanin na Salamatou ke bai wa matasa shi ne horo ga wadanda da suke da sha'awar bude nasu kamfanin.

Sauti da bidiyo akan labarin