Mata dogarai a fadar sarkin Dogarawa
September 10, 2018Talla
Matan ne dai suka nuna sha'awarsu ga shiga aikin na dogari a fadar masarautar garin Dogarawa da ke cikin jihar Tahoua. Sanin kowa ne dai a kasar Haussa Dogarai suke da alhakin kula da kare lafiyar sarakuna da ma kamowa, tare da gurfanar da mai laifi a fadar sarki. Baya ga haka mafi akasarin dogaran, kan kasance maza yayin da mata ke yin aiki na jakadiya. Sai dai a garin na Dogarawa da ke Jamhuriyar Nijar, matan sun zaburo tare da shiga wannan aiki na dogari, inda aka samu matan da suka kasance dogarai a fadar sarkin Dogarawa da ke Jamhuriyar Nijar.