1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar: Makaho mai tukin amalanke da sana'ar salula

November 23, 2016

Ibrahim Mansur ya samu nakasar makafta a sakamakon kamuwa da cutar dussa tun yana dan shekaru biyar a duniya, amma ya rungumi hanyar yin sana'a a maimakon bara.

https://p.dw.com/p/2T7K0
Blinder Mann Afrika
Hoto: AFP/Getty Images

A yankin Damagaram na Jamhuriyar Niger wani matashin makafo ne mai sunan Ibrahim Mansur  dan shekaru 25 da haihuwa Allah ya hore ma baiwa ta iya tukin amalanke da kuma sana'ar aikawa da kudi a wayar salula da ake kira shap-shap a kasar ta Nijar, sana’ar da a wani lokaci ma take gagarar masu idanu.

 

Shi dai Ibrahim Mansur matashin makaho ne dan asalin garin Geza Mahaman da ke a cikin karamar gundumar Mirriah da ke a yankin Damagaram. Ya samu nakasar makafta ne a sakamakon kamuwa da cutar dussa ko tininim tun yana dan shekaru biyar a duniya. Amma duk da haka a yanzu Allah ya yi masa baiwa ta iya gudanar da ayyuka daban-daban da suka hada da sana'ar aika kudi a salula gami da yin dashen layi.

Integration von Behinderten in Afrika Chemielehrer Anteneh Tarekegn
Hoto: DW/J. Jeffrey

 

A kuma matsayinsa na mazaunin karkara  yana gudanar da aikace aikacen gida ta hanyar jan amalanken shanu da kai taki gona don samun dan na sakawa a bakin salati da nufin kauracewa shiga bara kamar yadda ga al'ada makafi ke yi a kasashen Afirka da dama. Jama'a da dama ne a garin na Damagaram ke mu'amala da makahon a cikin aikin nasa dama nuna mamakinsu dangane da baiwar da Allah ya huwace masa. Sun kuma bayyana gamsuwarsu dangane da yadda ya kama wannan hanya a maimakon yin bara.