1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jam'iyyar Lumana ta sami shugaban riko

August 5, 2020

Wata kotu a birnin Yamai na Jamhuriyar Nijar ta bayar da umarnin a ba Noma Ummaru shugabancin riko na jam’iyyar Lumana Afirka ta Hamma Amadou.

https://p.dw.com/p/3gSBa
Niger Sitz der Fraktion der Oppositionspartei Moden Fa Lumana
Hoto: DW/D. Köpp

Kaiduka Abuba jigo a wani tsagi na jam'iyyar ta Lumana ya ce ba su ji dadin hukuncin ba, amma duk da haka yana fatan jam'iyyar za ta girgije kuma ta tunkari zaben kasar cikin nasara.

Wakilinmu na Yamai Mamman Kanta ya ce jam’yyar ta Lumana Afirka ta kwashe watanni tana fama da rikicin cikin gida a kan wanda ya kamata ya jagorance ta, abin ma ke nan da tun farko ya sa masu jayayya da juna a cikin jam’iyyar suka nufi kotu.