1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar: kwanaki 500 da sace ‘yan matan Ngalewa

November 15, 2018

A Jamhuriyar Nijar an cika kwanaki 500 da wasu 'yan bindiga da wadanda ba a san ko su wanene ba suka sace 'yan mata da yara kanana a garin Inglewa a jihar Diffa

https://p.dw.com/p/38Lcw
Niger Flüchtlinge aus Nigeria
Hoto: DW/A. Cascais

Yau kwanaki 500 kenan cif da 'yan kungiyar Boko Haram suka sace yara da yan mata ‘yan makaranta su 39 a garin Inglelewa dake cikin jihar Diffa har yanzu babu labarin su.

A ranar 2 ga watan Yulin 2017 ne ‘yan kungiyar ta Boko Haram suka shiga garin na Inglelewa suka bude wuta na harin kan mai uwa da wabi inda suka hallaka akalla mutum tara sannnan suka yi awon gaba da mata da kananan yara ciki har da dan wata tara da haihuwa.

Shugabannin kungiyoyin farar hulla dake rajin kare hakin dan Adam sun zargi hukumomin Nijar da rashin hanzarin neman ceto wadannan mata da yara.

A yayin wani taron manema labarai da suka kira a birnin Yamai Kaka Toda na kungiyar Alternative ya bukaci gwamnati ta yi koyi da hukumomin Najeriya wajen tattaunawa da wadanda suka yi garkuwa da yara domin a sako su.

Su ma dangi da iyayen yaran sun yi kira ga gwamnati ta dube su da idon rahama wajen kokarin ceto ‘yayan nasu.

Sai dai ministan cikin gida Malam Bazoum Mouhammed yace gwamnati na bakin kokari. Ya roki jama'a su kara taimakawa da addu'a har Allah ya sa a cimma nasara.