Nijar: Jam′iyyar MNSD ta shiga gwamnati | Labarai | DW | 14.08.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Nijar: Jam'iyyar MNSD ta shiga gwamnati

Bayan dogon lokaci da aka dauka ana yada jita-jita kan wannan batu, ta tabbata cewa kwamitin koli na jam'iyyar MNSD Nassara mai adawa a Jamhuriyar Niyar ya yanke shararar shiga gwamnati.

Niger Wahlen Seini Oumarou

Alhaji Seini Oumarou shugaban jam'iyyar MNSD Nassara a Nijar

Jam'iyyar ta MNSD Nassara karkashin jagorancin Alhaji Seini Oumarou da ke cikin kawancen jam'iyun adawa dai, ta amince za ta shiga gwamantin Shugaba Issoufou Mahamadou bayan kiran da shugaban kasar ya yi tayin kafa gwamnatin hadaka, cikin jawabinsa na bikin tunawa da ranar da Jamhuriyar ta Nijar ta samu 'yancin kanta daga Turawan mulkin mallaka na Faransa. Jam'iyyar ta MNSD ta bayyana wannan kudiri nata ne dai bayan wani taron muhawara da wakilan jam'iyyar da suka fito daga jihohin kasar suka gudanar a Yamai babban birnin kasar, inda mambobin kwamitin kolin jama'iyyar 148 daga cikin 203 suka halarci taron, kana 144 suka amince da matakin.