Nijar: Hukumar zabe ta sauya matsayinta | Labarai | DW | 25.07.2020
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Nijar: Hukumar zabe ta sauya matsayinta

Za a gudanar zaben shugabanin kananan hukumomi a Jamhuriyar Nijar, kafin na shugaban kasa kamar yadda hukumar ta ambata tun da farko, ko da yake ta musanta zarge-zargen bangaren adawa.

A karon farko hukumar zaben Jamhuriyar ta Nijar CENI, ta mayar da cikeken martani kan zargin da 'yan adawa suka yi mata, na hada baki da masu mulkin kasar domin tabka magudi a yayin manyan zabukan da ke tafe.

Tun da fari dai hukumar zaben ta Nijar wato CENI, ta bayyana ranar 13 ga watan Disamban da ke tafe a matsayin ranar da za a gudanar da zaben kananan hukumomi kamar yadda mafi yawan jam'iyyun siyasa har ma da na adawa suka bukata.