1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar: An kashe sojoji a yankin Tillaberi

Binta Aliyu Zurmi
August 2, 2021

Sojojin Nijar 15 sun mutu wasu 7 sun sami munanan raunuka a wani harin ta'addanci a yanklin Tillaberi.

https://p.dw.com/p/3yPyY
Burkina Faso | Übung Truppen aus Afrika
Hoto: picture-alliance/Zuma/Planet Pix/D. White

Ma'aikatar tsaro a Jamhuriyar Nijar ta sanar da mutuwar sojojinta 15, wasu sojojin bakwai kuma sun sami munanan raunuka yayin da ake ci gaba da neman wasu shida bayan wani harin ta'addanci da ya rutsa da su a yankin Tillaberi da ke kudu maso yammacin kasar da ke iyaka da kasar Burkina Faso.

Sanarwar ta kara da cewar ko baya ga harin kwantan baunar da 'yan ta'addan suka yi wa sojojin sun kuma dasa musu bama-bamai da suka tashi dasu a lokacin da suke kokarin kwashe wadanda suka jikkata.

Yankin na Tillaberi da ke kan iyakar kasashen Burkina Faso da Mali na fuskantar hare-haren mayakan jihadi na reshen IS a yankin Sahel da kuma reshen da ke mubaya'a ga kungiyar Al-Qa'ida.

Duk da sojojin hadaka na kasashen G5 sahel da ke jibge a wannan yankin, mayakan da ke gwagwarmaya da makamai na ci gaba da kashe al'umma da kuma jami'an tsaro.