Nijar: Dan farar hula zai takarar shugabanci | Siyasa | DW | 03.07.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Nijar: Dan farar hula zai takarar shugabanci

Wannan dai shi ne karon farko da wani dan kasar kuma ma dan farar hula ya fito ya bayyana wannan manufa a yayin da hankali ya karkata ga wanda zai maye gurbin shugaban kasa a 2021.

A Jamhuriyar Nijar shugaban rukunin kungiyoyin fararen hula na MPCR ne Malam Nouhou Arzika ya bayyana manufarsa ta kalubalantar 'yan siyasa a zaben shugabancin kasa na 2021 masu zuwa. Wannan dai shi ne karonsa na farko kenan da shugaban rukunin kungiyoyin fararen hular Nouhou Mahamadou Arzika ke nuna sha'awarsa ta tsayawa takarar shugabancin kasa a shekarar 2021 mai zuwa bisa abin da ya kira la'akarin da yayi na kasawar daukacin yan siyasar kasar da ke mulkin kasar yau tsawon shekaru fiye da 25, tun bayan gagarumin taro na kasa da ake kira Conference Nationale.

A yayin wata hira da tashar DW Nouhou Arzika ya bayyana muhimman dalilan  da suka kai shi ga daukar irin wannan matsayi: Ya ce 'yan siyasa in suka ce za su yi kuda yau she daukar alkawali ne suke amma gurinsu daban yake duk su suka bata guri da demokradiyar da muke so yanzu ta kulle, ai munga kamun ludden kowa ga matsayinsu ga irin yadda suka kaimu har yanzu komai na tauye.

To ko da wace manufa ce Nouhoun zai tunkarin zaben da ita? Ga abin da ya ke cewa: Matsayin mu na 'yan kasa muna da iznin yin takara ko ta shugaban kasa ko dan majalisa ko kananan hukumomi, kenan idan lokaci ya yi kenan zamu shiga cikin takarar don jama'a su gane da cewar kafin wannan lokacin ga matsayin da muke dauka tare da duk wani mai yin takara wanda idan muka je a gaban jam'a za mu kada shi.

Sai tuni tun ba'a je ko ina ba bangarori da dama ke cigaba da tofa albarkacin bakinsu game da yunkurin dan farar hullar na shiga gwagwarmayar yin zabe ga jam'iyyar PNDS Tarayya mai mulkin kasar  ayyana manufar ta Nouhou Mahamadou Arzika ba abin mamaki ba ne.

Sai dai ko baya ga jam'iyyun siyasa ra'ayi ya banbanta hatta ma a bangaren kungiyoyin farar hulla inda wasu ke ganin matsayin na Nouhou ya cancanta, wasunsu kuwa na masu ganin cewar lokaci ya yi da ya kamata a furta kalaman a cikin natsuwa da kwanciyar hankali don a gudu tare a kuma tsira tare. Malam Lawali Adamou wani dan fafatuka ne na kungiyoyin farar hulla a Jamhuriyar Nijar ya ce shin shi wai ya yi nazarin tsarin aza takarar shin mai ya tanada kuma wace irin shawara ya yi da danginshi 'yan farar hulla don a gudu tare a tsira tare.

Sai dai duk da wannan matsayi Nouhou ya ce ba abin da zai sa yayi sanyi a gwiwa musamman ma game da manufarsa na tunkarar 'yan siyasar duba da wani abin da ya kira gatse da wasu hukumomin kasar na koli suka yiwa 'yan farar hulla a baya kan samun wakilcin jama'a.

Sauti da bidiyo akan labarin