1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar: Bakin haure na ci gaba da mutuwa a sahara

Abdoulaye Mamane Amadou
June 27, 2017

Masu sharihi a Jamhuriyar Nijar na nuna damuwarsu kan yawan samun masu mutuwa a dajin sahara ta Agadez, inda masu kokarin zuwa kasar Libiya da zummar ficewa zuwa Turai ke gamuwa da ajalinsu.

https://p.dw.com/p/2fULy
Niger Agadez Bild 1 Konvoi mit Migranten verlässt Agadez
Motocin 'yan ci-rani a NijarHoto: DW/A. Kriesch/J.-P. Scholz


Hadarin dai na daga cikin irinsa mafi muni da yafi a kirga da sahara ke haifarwa bisa yunkurin jama'ar da ke rasa shi walau  da nufin zuwa Turai ko kuwa zuwa kasashen Larabawa don ci-rani. Sai dai wani abin cikas da ke cigaba da tayar da hankalin jam'a shi ne irin yanda mutuwar mutanen a sahara ke kara kamari duk da dokar da gwamnatin kasar ta dauka wace majalisar dokoki ta rattaba wa hannu a farkon shekara ta 2015 da ke ba hukumomin damar daukar matakin hukunci ga wadanda aka kama da yunkurin tsallaka bakin haure ta barauniyar hanya daga kasar.

Ga masu sharhi a kan al'aurran yau da kullum lamarin ya yi kamari ne sakamakon tsaurara hukuncin da gwamnati ta Nijar ta yi ba tare da daukar wasu matakai a daura da hakan ba. Malam Moussa Tchangari jagoran kungiyoyin fararen hulla na "Alternative Espace Citoyen" a Nijar ya ce  "tunda an hana bin hanyar da suka sani kenan jama'a za su rinka bin hanyoyin da ba'a sani ba kuma wadannan sabbin hanyoyin su ne ke tattare da hadaruka da za su sanya ko da sun bace ba za a iya gano su ba."

Duk wasu matakan da gwamnatin ta Nijar ke dauka na dakile aniyar ta 'yan ci-rani na daga cikin wasu hanyoyin na take-taken dokokin kasa da kasa da gwamnatin ke yi musamman ma na kasashen yammacin Afirka da Nijar din ta rattaba wa hannu inji Moussa Tchangari inda ya ke cewar ''Agadez ba iyakar kasashen Afirka ba ce da kasashen CEDEAO ko ECOWAS ba, kenan kamata ya yi a ce idan 'yan Aljeriya ne suka yi hakan ba laifi. To ta kaka Nijar za ta koma Agadez ta yi iyaka? Yin hakan na a matsayin sake maido iyakar mu daga Agadez don hana mutanen Nijar da na Afirka ta yamma su wuce kuma mun sa kasashen Turai sun kawo iyakar su a Agadez wannan ai bai dace ba.''

Wannan lamarin na mutuwar bakin haure akalla 50 da ceto wasu fiye da 20 na zuwa ne a yayin da ko a karshen watan mayun wannan shekarar jami'an tsaron kasar ta Nijar suka gano gawawakin mutane fiye da 40 a cikin sahara da suka ce kishirwa da rashin abinci ne sanadiyar mutuwar su. A ranar 25 ga watan Yuni ne dai hukumomin yankin Bilma a jihar Agadez suka fara samun labarin bacewar mutanen da aka ce sun kai su 70 da ke bisa wasu motocin masu fidda su inda aka ceto 20 daga cikinsu.

Niger Agadez Sahara Flüchtlinge
Irin motocin da ke daukan 'yan zuwa ci-rani daga Agadez a NijarHoto: Reuters/Akintunde Akinleye
Niger Agadez Sahara Flüchtlinge
'Yan gudun hijira masu kokarin zuwa kasashe irin su Libiya daga Agadez.Hoto: Reuters/Akintunde Akinleye
Niger Agadez Sahara Flüchtlinge Wasser
Masu kokarin zuwa ci-rani ta hanyoyin Sahara.Hoto: Reuters/Akintunde Akinleye