1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mutuwar sojoji: 'Yan Nijar na son a yi bincike

Salissou Boukari LMJ
January 16, 2020

A Jamhuriyar Nijar tun bayan harin 'yan ta'addan da ya yi sanadiyyar mutuwar sojojin kasar 89 a garin Chinagodar a ranar tara da wannan wata, al'umma da kungiyoyi ke aza ayar tambaya kan yadda sojoji da yawa suka halaka.

https://p.dw.com/p/3WK0E
Symbolbilder Niger Armee
Sojojin Nijar na fuskantar barazanaHoto: Getty Images/AFP/I. Sanogo

A cewar hukumar kare hakin dan Adam ta Nijar din CNDH, ta ce ya kyautu a gudanar da bincike domin gano musabbabin asarar rayukan sojojin na Nijar da aka yi a garin Chinagodrar sakamakon harin ta'addancin da kungiyar IS a yankin yammacin Afirboukariniger

ka ta dauki alhakin kai wa. Sai dai ya zuwa yanzu mutane na ci gaba da neman sanin yadda wannan lamari ya gudana har aka samu wannan babban adadi na sojojin da suka rigamu gidan gaskiya. Wannan batu dai ya mamaye kafofin sadarwa na zamani, inda wasu ke ganin kuskure ne na jiragen yakin abokan huldar kasa a fannin tsaro ko matsalar sadarwa a tsakanin masu fada a ji. Sai dai har yanzu babu wani haske kan yadda wannan lamari ya gudana.

Gwamnati ta yi bincike

Abas Abdoulmoumouni, masani ne kan harkokin tsaro da tsattsauran ra'ayi a yammacin Afirka, ya kuma ce babban abin da ake jira shi ne gwamnati ta fito ta yi karin haske domin gujewa yaduwar jita-jita. Daga nata bangare hukumar kare hakin dan Adam ta kasa wato CNDH, kira ta yi ga gwamnatin da ta aiwatar da bincike domin sanin yadda sojojin na Nijar masu tarin yawa suka mutu. Abin jira agani dai shi ne yadda gwamnatin za ta bullowa wannan lamari, ganin yadda al'umma suka tsaya a kan bakansu na neman sanin cikakken bayani kan mutuar sojojin na Nijar a garin Chinagodrar da Inates, inda ake furta kalamai mabambanta kan yaddahare-haren suka gudana.