Nijar: Ana kashe kudi ga malaman bogi | Labarai | DW | 20.09.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Nijar: Ana kashe kudi ga malaman bogi

Wannan fallasa dai na zuwa ne kwana guda bayan da malamai da dalibai suka kaddamar da yajin aiki na mako guda saboda rashin biyan albashi da ma kudin tallafi.

Oberschüler in Tahoua, Niger

Dalibai a makarantun Nijar na cikin garari

Jamhuriyar Nijar da ake bayyanata a matsayin kasa da ke fama da talauci cikin kasashen duniya na asarar sama da Euro miliyan hudu a kowane wata saboda biyan malamai da ba su a zahiri, kamar yadda hukumar da ke yaki da cin hanci da rashawa a kasar ta bayyana a ranar Talatan nan.Wannan fallasa dai na zuwa ne kwana guda bayan da malamai da dalibai suka kaddamar da yajin aiki na mako guda saboda rashin biyan albashi da ma kudin tallafi ko scholarships da ake ba wa daliban.

Salissou Oubandona da ke zama na biyu cikin jami'an hukumar yaki da cin hanci ta HALCIA ya ce bincike da suka gudanar daga makaranta zuwa makaranta ya gano cewa akwai sama da malaman bogi 1,900, sannan akwai sunayen wasu sama da dari shida da ke bayyana sau biyu ko uku cikin tsarin biyan albashi.

Ministan ilimi a kasar Mohamed Ben Omar ya amince cewar akwai matsala wajen biyan malaman makarantar da mafi yawa ke zama 'yan kwantiragi sai dai kawowa yanzu an warware matsalar.