Nijar: An haramta zanga-zangar kungiyoyin farar hula | Labarai | DW | 20.05.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Nijar: An haramta zanga-zangar kungiyoyin farar hula

Wannan dai shi ne karo na biyu da hukumomin ke hana yunkurin kungiyoyin na fararen hula da suka bukaci fitowar don yin zanga-zangar lumana.

Hukumomi a Jamhuriyar Nijar sun haramta wata zanga-zangar lumana da wasu kungiyoyin fararen hula suka kira da zummar nuna rashin jin dadin su kan yadda al'amura ke tafiya a kasar, musamman ma game da batutuwan da ke addabar kasar na cin hanci da rashuwa da rashin iya jagoranci da tabarbarewar ilimi da kame-kamen jama'a. Hukumomin dai da suka hana zanga-zangar sun bayar da dalilian tsaro a kan manya-manyan dalilan da suka hana ba da izinin yin gangami.