Nijar: An halaka 'yan ta'adda 15 kan iyaka da Mali
December 30, 2018Ministan tsaron kasar ta Nijar ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwar da ya fitar a wannan Asabar inda ya ce sojin kasa na kasashen biyu a bisa rakiyar jiragen helikofta da na yaki ne suka kai farmakin a yankin Arewa maso yammacin kauyen Tongo-Tongo na jihar Tillaberi inda sojojin Nijar biyar da na Amirka hudu suka halaka a cikin wani harin da 'yan ta'addan suka kai masu a watan Oktoban 2017.
A yayin farmakin sojojin kasashen biyu na Nijar da Faransa sun yi nasarar kwace wurare da dama na fakewar 'yan ta'addan tare da karbo baburra kimanin 20 da bindigogi 26 da tarin harsasai. Sanarwar ta ce ba a samu asarar ray ko daya ba daga bangare sojojin kasashen biyu a cikin wannan farmakin wanda sojojin suka kai a cikin daren Alhamis washe garin Juma'ar da ta gata.