Nijar: An fara zaben gama-gari | Siyasa | DW | 19.02.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Nijar: An fara zaben gama-gari

Al'ummar Nijar sun fara kada kuri'a a zaben shugaban kasa da na 'yan majalisar dokoki. Shugaban kasar Issoufou Mahamadou na nema wani sabon wa'adi na shekaru biyar.

Hukumar zaben kasar ta ce CENI ta ce tuni ta kammala dukannin shirye-shirye suka kammala domin gudanar da zaben cikin tsari yayin da jami'an tsaro suka ce sun dauki matakai na tabbatar da tsaro a fadin kasar.

Wakiliyarmu da birnin Gaya Ramatou Issa Ouanke ta ce tuni jama'a suka fara fita rumfunan zabe don kada kuri'unsu. Mata na daga cikin wanda suka fi fita wajen kada kuri'ar kamar yadda wakiliyar tamu ta shaidar.

Rahotanni daga Damagaram na cewar jama'a sun fita domin yin zaben kamar sauran takwarorinsu da ke sauran yankuna. Can a yankin Diffa da ke fama da tashin hankali na 'yan Boko Haram ma an fara zaben kuma labarin da muke samu ya zuwa yanzu babu wani tashin hankali.