Nigeria: ′Yan mata 110 sun bace a Dapchi | Labarai | DW | 25.02.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Nigeria: 'Yan mata 110 sun bace a Dapchi

Gwamnatin Najeriya ta bada alkaluman yara 'yan mata 'yan makarantar Dapchi a jihar Yobe wadanda har yanzu ba a gano su ba bayan harin Boko Haram.

Nigeria Dapchi Schülerinnen nach Boko-Haram-Angriff auf Schule vermisst (Reuters/O. Lanre)

Ministan yada labaran Najeriya Alhaji Lai Mohammed a makarantar 'yan mata ta Dapchi, Yobe

Gwamnatin Najeriya ta tabbatar da bacewar yara 'yan mata 'yan makarantar sakadaren kimiyya dake Dapchi a jihar Yobe bayan harin da 'yan Boko Haram suka kai hari makarantar a ranar Litinin da ta gabata inda suka yi awon gaba da dalibai da dama 

Ministan yada labaran kasar Lai Mohammed a cikin wata sanarwa da ya fitar yace a kididdigar da suka yi daga cikin yara 'yan makarantar su 906 an tantance yara 110 wadanda har yanzu ba'a gano su ba.

Tun da farko a jiya Asabar Iyayen yara 'yan makarantar sun baiyana sunaye 105 na 'ya'yansu mata wadanda suka ce har yanzu babu labarinsu, kusan mako guda bayan da 'yan Boko Haram suka kai hari makarantar.

Kawo yanzu dai babu tabbas a game da makomar yaran.