1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dole gwamnati ta dmagance matsalar fyade

Uwais Abubakar Idris
June 5, 2020

Kungiyoyin kare hakkin mata a Najeriya sun gudanar da zanga-zangar lumana a gaban hedikwatar ‘yan sandan kasar da ke Abuja, don nuna bacin rai da karuwar fyade da ake yi wa mata

https://p.dw.com/p/3dJst
Nigeria Demonstration Bring Back Our Girls in Chibok
Hoto: Reuters/A. Akinleye

Kungiyoyin matan sun bayyana takaici game da yawatar fyade da ake yi wa mata a kasar. Wannan fitina ta karu a kasar tun daga lokacin da aka kafa dokar zaman gida saboda annobar corona.

Daya bayan daya an rinka kiran sunayen matan da suka ce an yi masu fyade da suka ce ya haura 80. Malama Hafsat Shuaibu da ta yi takaka daga kauyen Dakwa a gefen Abuja  ta abin yana daga masu hankali.

Masu zanga-zangar sun bukaci gwamnatin Najeriyar ta kafa dokar ta baci tare da yin kira ga hukumar ‘yan sanda da kotuna Najeriyar su nuna cewar da gaske suke yi wajen kare mutuncin mata da hukunta wadanda ake cin zarafinsu kamar yadda Hajiya Saudat Mahdi shugabar kungiyar kare hakkin mata da tabbatar da ganin an yi masu adalci ta baiyana.

Nigeria Protest
Hoto: picture-alliance/AP Photo

Kakakin rundunar ‘yan sandan Najeriyar Frank Mba ya yiwa masu zanga zangar bayani yana bada tabbacin cewa suna daukar matakai don shawo kan matsalar.

Yace mun fahimci irin halin takaici da ya sanya ku fitowa wannan zanga-zanga, amma ku sani duk wani dan sanda da kuka gani to mace ce ta haife shi, kuma ko dai yana da mata ko kanwa, don haka burinmu ne mu yi aiki tare da ku don gani babu wata mata da aka yiwa fyade, zamu kara matsa kaimi soai.

Amma ga Niri Guyat ta kungiyar Action Aid tace akwai bukatar fahimtar lalacewar lamarin a yanzu.

Za’a sa ido a ga matakin da za’a dauka don zama darasi ga na baya a dai dai lokacin da matsalar fyaden ke ci gaba da karuwa wadda ake danganatawa da rashin hukunta masu aikata wannan laifi a Najeriya.