Niger Delta: Jan kafa kan aikin gyaran muhalli | BATUTUWA | DW | 20.12.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

BATUTUWA

Niger Delta: Jan kafa kan aikin gyaran muhalli

Al'ummar Ogoni sun gudanar da gangami don yin adawa da matakin gwamnatin Najeriya na bai wa kamfanoni damar dawo da ayyukan hakar mai a yankin da kuma jan kafar da ake a aikin gyaran muhallin da kamfanonin suka gurbata.

Zanga-zangar ta wannan Laraba (20.12.2017) da wasu daga cikin al'ummar Ogonin suka gudanar ta hada da maza da mata da yara dama tsofaffi inda suka yi jerin gwano a kan titin Moscow Road wato harabar ofishin kamfanin man NNPC  don baiyana kokensu. Zanga- zangar dai ba ta samu tsaiko ba ko kadan daga jami'an tsaro kuma wani abin lura babu wani jami'i daga kamfanin na NNPC da ya fito dan yi wa masu zanga-zangar jawabi.

Shell Öl Umweltverschmutzung Niger River Delta in Nigeria (Getty Images)

Malalar mai ta yi sanadin gurbata ruwa da kuma gonaki a yankin Niger Delta na Najeriya

Shekaru biyar da suka gabata, sashen kula da muhalli na Majalisar Dinkin Duniya ya sanar da kammala aikin tantance halin gurbacewar da yankin na Ogoni ya yi a sakamakon tsiyayar danyan mai na kamfanonin da ke aikin hakar suka yi tare da mika wa gwamnatin kasar sakamakon aikin tantancewar amma jan kafar da aka yi ta yi a gyaran muhallin ya haifar da cece-kuce musamman lokacin da tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan daya fito daga yanki ya ke kuma jan ragamar kasar.

Gwamnatin Muhammadu Buhari a yanzu ta tabbatar da cewar za ta gudanar da aiki amman fa sannu a hankali za a yi shi don tabbatar da cewar an yi abin da ya kamata. Ga dukkan alamu hakan bai yi wa al'ummar dadi ba ganin matakin da suka dauka na sake yin kira ga gwamnati ta hanyar gudanar da zanga-zangar da kuma yin adawa da damar da aka bai wa kamfanoni aikin hakar mai ba tare da an cika musu alkawuran da aka daukar musu a baya ba.

 

Sauti da bidiyo akan labarin