Nicolas Sarkozy na fuskantar bincike | Labarai | DW | 02.07.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Nicolas Sarkozy na fuskantar bincike

Mahukuntan Faransa na zargin tsohon shugaban ƙasar da aikata almundahana da kuɗaɗen al'umma a yayin mulkinsa.

Tsohon shugaban ƙasar ta Faransa dai Nicolas Sarkozy ya musanta zargin da ake masa. A wata hira da ya yi da gidan radiyon "Europe 1" Sarkozy ya zargi fannin shari'a na ƙasar da zama ɗan amshin shatar gwamnati ta yadda ake amfani da shi domin cimma wani ɓuri na siyasa.

Nicolas Sarkozy ya ƙara da cewar shi kam bai taɓa cin amanar 'yan ƙasar sa ba kuma bai taɓa aikata wani abu da ya saɓawa dokokin ƙasar da kuma tanade-tanaden tsarin mulkin Faransa ba. Mahukuntan ƙasar ta Faransa dai sun ƙaddamar da fara yin bincike a kan tsohon shugaban ƙasar Nicolas Sarkozy bayan da suka zarge shi da aikata almundahana da kuɗaɗen jama'a a yayin da yake kan karagar mulki.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita Abdourahamane Hassane