Nicolas Maduro ya lashe zaben shugaban kasar Venezuela | Labarai | DW | 15.04.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Nicolas Maduro ya lashe zaben shugaban kasar Venezuela

Wanda marigayi tsohon shugaban Venezuela Hugo Chavez ya zaba da ya gaje shi ya lashe zaben shugaban kasar amma ba da wata rata mai yawa ba.

Nicolas Maduro ya doke abokin hamayyarsa Henrique Capriles Radonski. Sanarwar da hukumar zaben kasar ta bayar ta nunar da cewa Maduro ya lashe zaben ne da kashi 50 da digo 66 daga cikin dari akan kuri'u na kashi 49 da kusan digo daya da abokin hamayyar nasa Capriles ya samu. Kenan ko da yake ba su samu kuri'un da za su kai su ga rike madafun iko ba, za a iya cewa 'yan adawa sun samu ci-gaba da kusan kashi biyar daga cikin dari idan aka kwatanta da zaben Okotoban bara. Kashi 78 daga cikin dari na wadanda suka cancanci kada kuri'a ne suka shiga zaben.

Shi dai Maduro mai shekaru 50 da haifuwa wanda ya taba rike mukamin ministan harkokin waje, babu shakka zai ci gaba da bin tafarkin kwaminisanci a wannan kasa mai arzikin man fetur. Zai kuma ci gaba da rike ragamar shugabancin kasar har ya zuwa shekarar 2019.

To sai dai a wani ci-gaban kuma Henrique Capriles ya kalubalanci sakamakon zaben da cewa nasu sakamakon ya sha ban ban da wanda hukumar zaben kasar ta bayar.

Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas
Edita: Mohammad Nasiru Awal