1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Tarihi

Ngungunyane, Sarkin da ya yaki mulkin mallakar Portugal

Abdourahamane Hassane USU
March 28, 2018

Sarki na karshe na Gaza, ya yaki mulkin mallaka na Portugal, karni daya bayan mutuwarsa Ngungunyane ya zama jarumin da ya jurewa ‚yan mulkin mallaka.

https://p.dw.com/p/2v9DV
Ngungunyane
Hoto: Comic Republic

Yaushe kuma ina Ngungunyane ya rayu?  

Ngungunyane sunansa na haifuwa shi ne Mudungazi, an haife shi a shekara ta 1850 a daular Gaza, a kudu maso gabashin Afirka. Kakansa Manukuse ya mallaki baki dayan yanki, tsakanin kogin Zambes da ke a kudu maso gabashin tekun Indiya, wadda a yau ita ce kasar Mozambik. Shi ne sarkin Gaza na karshe kafin turawan mulkin mallaka na Portugal su ci daularsa da yaki. Ya mutu a ranar 23 ga watan Disamban shekara ta 1906.

 

Yaya Ngungunyane ya samu mulki? 

Bayan mutuwar kakansa Manukuse a 1858 yakin da aka yi tsakanin magada biyu Muzila shi ne ya yi nasara tare da tallafin hukumomin Portugal.  Muzila da matarsa Yosio Mudungazi ya sa an kashe daya daga cikin ‘yan uwansa kana ya ayyana kansa a matsayi sarki a 1884. Ya canza sunansa zuwa Ngungunyane, gagararre. Shekaru 11 ya yi yana mulki, ya kuma rika uzurawa al‘ummarsa.

 

Yaya Ngungunyane ya yi hulda da Turawa?

Ngungunyane ya samu mulki watanni kalilan kafin babban taron Berlin na shekara (1884-1885) lokacin da Turawa suka raba Afirka. A game da bukatar Jamus da Birtaniya na samun Mozambik, sannan ga Portugal. Da yake ya gane akwai jayayya tsakanin kasashen Turai a kan batun ya yi amfani da wannan dama don jan hakalin Birtaniya da Portugal.

Bayanin Sarki Ngungunyane da bijirewa Turawan mulkin mallaka a Angola

Yaya aka samu nasara a kan  Ngungunyane?

A farkon shekarar 1895, Antonio Eanes babban kwamishina na Mozambik ya ba da umarnin kai wa Ngungunyane hari, lokacin ma da yawa daga cikin al'ummarsa sun dawo daga rakiyarsa. An yaki daularsa da karfi cikin jini bayan yake-yaken Coolela da Mandlakasi. Ngungunyane ya tsere izuwa Chaimite, inda aka bizne kakansa. A ranar 28 ga watan Disamba na shekara ta 1895 wakilin gwamnatin Portugal a Gaza, Mouzinho de Abuquerque, ya sa an kulle shi a gidan kurkuku, kana aka kai shi hijira a Lisbon tare da wasu mukarrabansa. Kuma an saka su ciki irin gidan kaji a Lisbon, kafin a baje kolinsu a wani gidan kallo. Ya kwashe tsawon rayuwarsa yana yin hijira. Ya koyi rubutu da karatu kana aka tilasta masa ya rungumi addinin Kirista a gidan kurkuku kafin aka saka masa suna Reinaldo Frederico Gungunhana. Zakin Gaza ya mutu da ciwon mutuwar rabin jiki a shekara ta 1906.

 

Yaya Ngungunyane ya zama jarumi da Mozambik take tunawa da shi?

Bayan bukatar Samora Machel tsohon shugaba kasar Mozambik na farko, bayan samun ‘yancin kai an dawo da gawar Ngungunyane a lokacin bikin cikar shekaru goma da Mozambik ta samu ‘yancin kai. Ga Frelimo kungiyar ‘yan kishin kasa wadda ta yi fafutukar neman ‘yancin kai a 1975 na Mozambik, Nguguyane jarumi ne. Samora Machel tsohon shugaba kasar Mozambik da shugaban FRELIMO na farko Eduardo Mondlane da tsohon shugaban Mozambik na biyu Joaquim Chissano su dukkaninsu 'yan yankin Gaza ne.

 

Wai Ngungunyane mutum ne da wasu ke yin tababa a kan jarumtakarsa:

Ana dai fadakar da matasan Mozambik tarihin Ngungunyane domin samun hadin kai, sai dai abin ba ya yin tasiri sakamakon yadda Ngungunyane ya rika fatattakar al'ummarsa. Albarkacin bikin cikar shekaru 100 na adawar da daular Gaza ta nuna, a 1995 shugaban kasar Mozambik Joaquim Chissano ya kaddamar da bikin girka wani gunki na Ngungunyane, amma lokaci kadan al'umma suka farfasa gunkin. Wannan na nuna irin yadda ake yin tababa a game da Ngungunyane, wanda wasu ke sonsa wasu ba sa kaunarsa.

 

Shiri na musamman "Tushen Afirka" aiki ne na hadin gwiwa tsakanin DW da Gidauniyar Gerda Henkel.