1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tsananta dokar mallakar bindiga a New Zealand

Abdul-raheem Hassan MNA
March 16, 2019

Wani mutum ya bayyana a gaban kotu a New Zealand inda ake tuhumarsa da laifin kisan-kai kwana daya bayan hari kan masallatai biyu a birnin Christchurch.

https://p.dw.com/p/3FAsh
Neuseeland | Anschlag von Christchurch | Brenton Tarrant
Hoto: Reuters/M. Mitchell

Firaministar New Zealand Jacinda Ardern ta sha alwashin tsananta dokokin mallakar bindiga a kasar bayan gano maharin da ya kashe musulmai a masallaci na da bindigogi har guda biyar da ya yi amfani da su wajen kai harin.

Hukumomin New Zealand sun tabbatar da cewa maharin mai shekaru 28 farar fata dan kasar Ostireliya mai akidar kyamar baki, ya kuma samu lasisin mallakar bindiga a watan Nuwamban shekarar 2007 da niyyar daukar fansa kan musulmai.

Mutane 49 suka rasu a harin bayan da dan bindigar ya bude wuta kan mai uwa da wabi a cikin masallatai, yayin sallar Juma'a. Jami'an 'yan sanda na ci gaba da bincike don gano sauran masu hannu a kai harin.

Kawo yanzu an fara tantance 'yan kasashen waje da suka mutu a harin, ciki har da 'yan kasar Masar guda hudu.

Shugabannin duniya na ci gaba da Allah wadai da harin da ke zama mafi muni a kasar.