1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

New Zealand: Sabuwar gwamnati sai da hadaka

Yusuf Bala Nayaya
September 23, 2017

A cewar Bill English lokacin da ya ke magana a ofishin kamfe na jam'iyyarsa a Auckland ya ce jam'iyyar ta National Party ta shirya fara tattaunawa da 'yan jam'iyyar New Zealand First.

https://p.dw.com/p/2kZX4
Neuseeland Wahl Premierminister Bill English
Hoto: picture-alliance/AP Photo/New Zealand Herald/D. Sherring

Shugaban jam'iyyar New Zealand National Party Bill English ya bayyana a ranar Asabar din nan cewa jam'iyyar 'yan kishin kasa ta New Zealand First Party na da rawar takawa wajen kafa sabuwar gwamnati a kasar bayan zaben 'yan majalisa mai zafi da aka yi a kasar. A cewar English lokacin da ya ke magana a ofishin kamfe na jam'iyyarsa a Auckland ya ce jam'iyyar ta National Party ta shirya fara tattaunawa da 'yan jam'iyyar New Zealand First a 'yan kwanaki da ke tafe.

Sakamakon zaben da ya fita bayan kirga sama da kashi 98 cikin dari na kuri'u ya nunar da cewa jam'iyyar ta National Party ta samu sama kashi 46 cikin dari yayin da jam'iyyar Labour da ke adawa ke da sama da kashi 35 cikin dari. Sakamako na karshe dai ciki kuwa har da kuri'u na 'wadanda ke zaune a kasashen waje zai bayyana a ranar bakwai ga watan Oktoba kamar yadda hukumar zaben New Zealand ta bayyana.