Netherlands ta amince ta kara yawan sojojinta a Afghanistan | Labarai | DW | 03.02.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Netherlands ta amince ta kara yawan sojojinta a Afghanistan

Kasar Netherlands zata tura karin dakaru zuwa Afghanistan, inda zasu yi aiki karkashin inuwar rundunar wanzar da zaman lafiya ta kungiyar NATO wato ISAF. FM NL Jan Peter Balkenende ya ce majalisar dokoki a birnin The Hague ta goyi da bayan wannan shiri na girke sojojin kasar su kimanin dubu daya zuwa dubu 1 da 400 zuwa yankuna masu hadari a kudancin Afghanistan. A halin da ake ciki kasar ta NL na da sojoji fiye da 620 da ke aiki a sassa dabam dabam na Afghanistan. To amma al´umar kasar na nuna adawa da tura sojojin zuwa Afghanista, bisa wannan dalili ne aka jinkirta yanke wannan shawara har tsawon makonni da dama. A bara kungiyar tsaro ta NATO ta amince ta kara yawan dakarunta a Afghanistan daga dubu 9 zuwa dubu 15.