Netanyahu zai kafa gwamnatin kawance a Isra′ila | Siyasa | DW | 23.01.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Netanyahu zai kafa gwamnatin kawance a Isra'ila

Sakamakon zaben bai yiwa Netanyahu dadi ba, saboda jam'iyarsa ta Likud-Beitanu kujeru 31 kawai ta samu daga cikin jimlar 120 gaba daya.

Ranar Talatar da ta gabata ne aka gudanar da zaben majalisar dokoki a kasar Isra'ila. Sakamakon da zaben ya haifar kuwa ya zama mai ban mamaki, saboda tsohon dan jaridar nan, Jair Lapid, ya dauki matsayi na biyu a karkashin tutar jam'iyarsa ta Jesch Atid, inda ya samu kujeru 19. To sai dai a daya hannun, zaben bai yiwa Pramiyan Netanyahu dadi ba, saboda jam'iyarsa ta Likud-Beitanu kujeru 31 kawai ta samu daga cikin jimlar 120 gaba daya.

Tsohon dan jarida, kuma ma'aikacin gidan telebijin na Isra'ila, Yair Lapid, ana iya cewar shi ne kadai mutumin da ya sami nasarar zaben na ranar Talata.

Yair Lapid

Yair Lapid, mutumin da ya samu gagarumar nasara a zaben

Lokacin bikin wannan nasara tare da magoya bayansa, dan siyasar, kuma shugaban jam'iyar Jesch Atid yace:

"Kasar Isra'ila yanzu dai tana kan hanyar fuskantar wani gagarumin kalubale. Mun kasance a wani yanayi na rikicin tattalin arziki, abin dake zama barazana ga ma'aikata da masu matsakaicin karfi a Isra'ila. Kasarmu tana fuskantar barazanar duniya za ta mai da ita saniyar ware. Hanya guda ta rage da za'a bi domin samun nasarar shawo kan wannan kalubale. Wannan hanya kuwa ita ce hada kai da hada karfi wuri guda."

Koma baya ga Netanyahu

Bayan da aka kammala kidaya kuri'u cikin dare, sakamakon da aka samu ya tabbatar da cewar Lapid ya sami kujeru 19 a majalisar dokoki ta Knesset mai kujeru 120 a cikinta. Mutumin da ya sha kaye a zaben na Talata shine Pirayim minista mai ci, Benjamin Netanyahu. Lokacin da ya baiyana gaban magoya bayan sa cikin dare, yace idan har ya sami damar kafa sabuwar gwamnati, yana da abubuwa biyar ne da yake da burin samun nasararsu:

"Abu na farko shi ne mu hana kasar Iran ta kera makaman nucear, sai hana fadi-tashin tattalin arzikin Israila da kara maida hankali a matakan samar da zaman lafiya a gabas ta tsakiya, musmaman da Falesdinawa da bullo da shirin aikin soja na bautawa kasa ga dalibai yan darikar orthodox da kuma rage tsadar rayuwa tsakanin 'yan Isra'ila."

Netanyahu ya ce burinsa shi ne ya kafa gwamnatin hadin gwiwa da zata kunshi jam'iyu masu yawa a cikinta, ya kuma nunar da cewar sakamakon da zaben ya haifar wata dama ce ta aiwatar da canje-canje da yan Israila suke bukata. Duk da haka, masana suka ce ganin yadda masu zabe suka nunawa shugaban gwamnatin iyakarsa, duk wasu shawarwari na neman kafa sabuwar gwamnati ba zasu zama masu sauki a gareshi ba. Netanyahu tilas ya tattauna da wani sabon dan siyasa a kasar ta Israila, wato Naftali Bennett, dake shugabancin jam'iyar Habait Hajehudi, wadda jam'iya ce mai matsanancin ra'ayin kishin Yakudanci, kuma mai kaunar ganin Israila taci gaba da zafafa manufofinta na kakkafa matsugunan Yahudawa a yankunan da ta mamaye, tare da hana Falesdinawa samun kasar kansu ko ta halin yaya.

Bukatar canji na hakika

Akwai kuma yan siyasar da ko da shi ke sun sami kujeru a majalisar dokokin, amma ba za su taka wata muhimmiyar rawa a siyasar kasar ba. Shugabar jam'iyar Labour Shelly Yachimovic tace za ta jira a sami sakamakon zaben gaba daya tukuna, kafin ta ga ko zai yiwu a sami canji na hakika da ake bukata.

Tzipi Livni Israel Opposition Kadima Partei

Tsipi Livni ta jam'iyar Kadima

Tsohuwar ministar harkokin waje, Tsipi Livni ta sami shiga majalisar dokoki da sabuwar jam'iyar da ta kafa, inda ake ganin ita kadai ce take goyon bayan ci gaba da tattaunawa da Palesdinawa. Jam'iyar Shas mai matsanancin ra'ayi na addini, tana iya zama jam''iyar da mulkin Israila ba zai yiwu ba sai da ita. Shugabanta Arie Deri yake cewa:

"Idan ka duba, zaka ga cewar jam'iyar Likud tayi asarar kujeru tsakanin 10 zuwa 11, jam'iyar Kadima ta bace baki daya. Wannan babbar nasara ce a garemu, domin kuwa jam'iyar Shas tana nan yadda aka santa. Na gamsu matuka, saboda nasarar da muka samu ba kadan bace."

Jam'iyar mai ra'ayin addini zata gamsu muddin ta shiga gwmanatin da za'a kafa, duk kuwa da sanin cewar masu zabe a ranar Talata, sun nuna cewar suna bukatar sabbin fuskoki a tsarin siyasar kasar ta Isra'ila.

Mawallafa: Christian Wagner / Umaru Aliyu
Edita: Mohammad Nasiru Awal

A kasa kuna iya sauraron sautin rahotanni kan wannan batu.

Sauti da bidiyo akan labarin