Netanyahu ya kaurace wa minista Gabriel..
April 25, 2017Firaminmistan Israila Benjamin Netanyahu ya soke ganawar da aka shirya a ranar Talatar nan tsakaninsa da Ministan harkokin wajen Jamus Sigmar Gabriel bayan da ministan na Jamus da ke ziyara a Israila ya tattauna da wasu kungiyoyi masu adawa da mamayar da Israila ta yiwa wasu yankunan Falasdinawa.
Wannan takaddamar da ta kunno kai dai na neman fadada rashin jituwa tsakanin Israilar da Jamus kan batun Falasdinawa.
Jamus dai na kara yin kakkausar suka ga manufofin gwamnatin Israila ta Benjamin Netanyahu na fadada matsgunai a yankunan da Falasdinawa ke son kafa kasarsu.
Yayin da ya kai ziyara birnin Ramallah a yankin gabar yamma, ministan harkokin wajen jamus Sigmar Gabriel ya gana da Firaministan Falasdinawa Rami Hamdallah, inda shugabannin biyu suka gudanar da taron manema labarai na hadin gwiwa.