1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kokarin sulhu da 'yan IPOB

June 24, 2021

Gwamnatin Najeriya na shirin bude tattaunawa da masu ruwa da tsaki a yankin Kudu maso Gabashin kasar game da tada kayar baya na 'yan kungiyar IPOB masu rajin farfado da Biafra

https://p.dw.com/p/3vINP
Nigeria pro-Donald-Trump-Kundgebung der Indigenous People of Biafra in Port Harcourt
Hoto: Getty Images/AFP

Ko bayan tada kayar bayan da ke neman jefa makomar yankin na Kudu maso Gabas cikin yanayi maras kyau dai, gwagwarmayar neman ballewar na kuma barazana har ga shi kansa babban zaben na shekaru Biyun da ke tafe.To sai dai kuma Abujar na neman sauyin rawa daga karfi na hatsi ya zuwa tattaunawa da nufin tunkarar rikicin dake tashi da nuna alamu na lafawa.

NIGERIA Biafra Aba Demonstration
Masu fafutukar neman BiafraHoto: Getty Images/AFP/P. U. Ekpei

Karin bayani: Najeriya: Za a tuhumi masu kai hari a Kudu maso Gabas da ta'addanci

Chris Ngige dai na zaman minista na kodagon tarrayar najeriyar, kuma daya a cikin dattawan yankin da ya gana da shugaban kasar, kuma ya ce Abujar ta amince da bude tattaunawar da ke da burin kai karshen matsalar mai tasiri. Ngigen da ya gana da shugaban kasar dai ya ce, Shugaba Buhari yayi lale da marhabin da batun tattaunawar da ke iya bude sabon babi a kokari na zaman lafiya cikin yankin.

Karin bayani: Umarnin da IPOB ta bayar ya karbu a Najeriya

" Mun kalli yanayin tsaro musamman ma a yankinmu na Kudu maso Gabas, kuma mun masa tayi bisa abun da al'ummar yanki da gwamnatoci ke da bukata. Muna shirin dorawa da batun tattaunawa, wanda kuma a karshe abun da zai faru ke nan. Dole ayi magana dole ne da a tattauna.  Bangaren tattaunawar zai fara daga gobe, ministan tsaro da na cikin gida da manyan hafsoshi na tsaro sun je Enugu a ranar Asabar din da ta shude, kuma zamu ci gaba kan wannan daga gobe. Mun yi wa shugaban kasa bayani, kuma ya amince cewar hanyar tattaunawar ita ce hanyar da ya kamata abi."

Nigeria Biafra | Nnamdi Kanu
Shugaban IPOB Nnamdi Kanu Hoto: DW/K. Gänsler

Duk da cewar dai har ya zuwa yanzu babu dalla dallar tsarin tattaunawar da ma tasirin da take iya kaiwa ga kokari na tabbatar da zama na lafiya a jihohin yankin guda biyar, akwai dai alamun daukaci na bangarorin da ke cikin rikicin dai  na nuna alamun gajiya da ganin sakamakon da ke kara fitowa fili daga yankin.