1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Neman warware rikicin Ukraine a siyasance

August 16, 2014

Shugaban China Xi Jinping ya bukaci da samo wata hanya a siyasance da za ai amfani da ita wajen warware rikicin da yanzu haka ke wakana a gabashin Ukraine.

https://p.dw.com/p/1Cvlc
Russland Ukraine russische Panzer an der Grenze bei Kamensk-Schachtinski
Hoto: Reuters

Kamfanin dillancin labaran China na Xinhua da ya rawaito wannan labarin ya ce Shugaba Xi ya bukaci hakan ne loakcin da sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon ya ziyarce shi inda ya kara da cewar gaggauta samo bakin zaren warware mastalar zai taimaka wajen magance cigaba da dagulewar lamura tsakanin kasashen biyu.

Wannan kira na shugaban na China dai na zuwa ne daidai lokacin da kasahsen duniya ke cigaba da nuna fargaba ta sake fadadar rikici tsakanin kasashen biyu wanda hakan ka iya jawo karawa Rashan tsauraran takunkumi na karya tattalin arzki.

China dai na dasawa matuka da Rasha ta fuskar tattalin arziki domin ko a kwanakin da suka gabata bangarorin biyu sun sanya hannu kan wata yarjejeniya ta cinikayyar isakar gas ta dalar Amirka miliyan dubu 400.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Zainab Mohammed Abubakar