1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Neman shawo kan rikicin addinai a kasashen ECOWAS

November 23, 2016

Taron neman magance rikicin addinai a cikin kasashen ECOWAS na birnin Yamai ya fitar da shawarwari na matakan rigakafin hana barkewar irin wadannan rigingimu masu haddasa asarar rayukan al'umma da dukiyoyi.

https://p.dw.com/p/2T8tt
Nigeria Proteste gegen den neuen Emir von Kano Sanusi Lamido Sanusi
Hoto: Amino Abubakar/AFP/Getty Images

 A Jamhuriyar Nijar an kammala zaman taro kan neman hanyoyin shinfida zaman lafiya tsakanin al'umma mabiya addinai da tafarkoki mabambanta, wadan kungiyar kula da tattalin arzikin kasashen afrika ta yamma wato CEDEAO ko ECOWAS ta shirya a karkashin jagorancin sarkin Musulmi Sokoto Sultan Sa'adu Abubakar na uku,da Cardinal na Abuja John Onaiyekan. 

Mahalarta taron wadanda suka fito daga kasashe daban-daban na Kungiyar ta ECOWAS sun tattauna tare da gabatar da jerin kasidu a kan dalilan da suke gani ke sa ana samun sabani tsakanin tsakanin addinai daban-daban da ke haifar da tashe-tashen hankula. Ko baya ga rikicinn da ake samu a wasu lokuttan a wasu kasashen tsakanin mabiya addinin Muslunci da na Kirista, akwai kuma wani rikicin da ake fuskanta a tsakanin mabiya darikoki da mazhabobi mabambanta a cikin addinan biyu. Taron ya gudanar da nazari da fitar da sabbin shawarwari  kan hanyoyin da ya kamata a bi a wajen dinke barakar da ke haddasa wadannan tashe-tashen hankula. Dr Khalid Aliyu Abubakar shi ne babban sakatare janar na babbar kungiyar Musulmin Najeriya ta Nasarul Islam:

Nigeria Abuja Sultan  Sokoto Sa'ad Abubakar III
Hoto: DW/N. Mahaman Kanta

" Abin da taron ya gano shi ne jahilci na daga cikin manyan al'amurran da ke barazana dama haddasar da matsalolin tsaro da ake fuskanta. Na biyu talauci da yi yi wa jama'a katutu na taka muhimmiyar rawa wajen rura wutar rikicin inda ake iya bai wa mutane masu talauci wani abin da ke taka kara ya karya ba ya jasu cikin tayar da tarzoma. Na ukku shi ne rashin ingancin shugabanci da yaduwar shugabanci na danniya da murdiya da sace kudaden da aka warewa domin gudanar da ayyukan kyautata rayuwar al'umma"

 Baya ga duk wadannan matsalolin da taron ya hango mahalarta taron sun dauki alkawarin daukar matakan da duk suka dace domin magance wadannan matsalolin
 
"A kan abin da aka tsayar shine yau duk kasashen nan na Afrika za'a yada ire iren wadannan bayyanai a kuma tabbatar da cewar an kaisu a ko ina a cikin birane da kauyuka, sannan ya kamata a ce kafin shekaru biyu na tafe ko wace kasa ta tabbatar da ta yi irin wannan taron a ko wace shekara a kuma tabbatar da adalci da gaskiya"

Nigeria Abuja Erzbischof John Onaiyekan
Hoto: DW/N. Mahaman Kanta

 Matasa dai su ne kanwa uwar gami game da duk wasu bukatocin da a ke son cimma musamman ma da suka shafi tashe-tashen hankali .A cewar Falmata Moctar daya daga cikin mahalarta taron,

"Kamata ya yi a duk wata bukatar da ta taso a saka matasa a gaba. Yau a dauki misali idan ma wani mukami jama'a suke bukata kamar magabata haka, dole ne sai an dauki matasa an saka su a gaba. Mune masu ihu masu barna masu rikici kenan idan an sakamu a cikin duk wasu harkokin wayar da kai domin son juna da son kasa to za'a samu galaba" 

Daga karshe dai taron ya dora wa mahalarta taron yada shawarwarin da taron ya cimma a tsakanin al'ummominsu mabiya ko wani addini da kwadayin za su yi tasiri a cikin zukatan al'umma wanda hakan zai taimaka ga samar da wanzuwar zaman lafiya a tsakanin al'umma.