1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Neman shawo kan matsalar tsaro a Bangui

April 16, 2013

Shugaban Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya Michel Djotodia ya sha alwashin magance matsalar tsaro da ke addabar kasarsa tun bayan hambarar da gwamnatin François Bozizé.

https://p.dw.com/p/18H1H
Hoto: picture alliance/landov

Sabon shugaban Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya Michel Djotodia ya bayyana matakan da zai yi amfani da su wajen kawo karshen matsalar tsaro da ta addabi babban birnin kasar. Ya ce zai jibge karin jami'an tsaro dubu a Bangui tare da mayar da mayakan kungiyar tawaye ta Seleka da ke kwasar ganima tare da cin zarafin jama'a barikin soje. Michel Djotodia wanda ya ayyana kansa a matsayin shugaban kasa bayan hambarar da Francois Bozize, ya kuma nuna yiwuwar neman gudunmawar sojoji daga Chadi domin taimaka masa mayar da doka da oda a cikin kasarsa.

Shugaban na Jamhuriyar Afirka ta tsakiya ya kuma ce zai samar da jami'an tsaro da za su kare rayuka da kuma dukiyoyin al'uma a dukkanin yankuna da kasar ta kunsa. Mutane sama da 20 ne dai suka rasa rayukansu a karshen mako a wani gumurzu da ya hada mayakan Seleka da ke kwasar ganima da kuma mazauna wasu ungwani biyu na Bangui babban birni. Kakakin gwamnatin Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya Crépin Mboli-Goumba ya yi kira ga kasashen yankin Afirka ta tsakiya da su taimakawa kasarsu magance wannan matsala ta rashin kyakkyawar tsaro.

Mawallafi: Mouhamadou Awal Balarabe
Edita: Yahouza Sadissou Madobi