Neman kafa gwamnatin kawance | Labarai | DW | 04.10.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Neman kafa gwamnatin kawance

Ana kan tattaunawa kan kafa gwamnati hadaka ta kasar Jamus.

Shugaban gwamnatin Jamus Angela Merkel da jam'iyyarta mai ra'ayin mazan jiya, sun fara tattaunawa da babbar jam'iyyar adawa ta SPD, kan kafa gwamnatin kawance, kwanaki 12 bayan gudanar da babban zabe na kasa baki daya.

Jam'iyya mai mulkin ta CDU ta samu kashi 41.5 cikin 100, yayin babbar jam'iyyar adawar ta samu kashi 25.7 cikin 100.

Tattaunawar da ake gudanarwa wannan Jumma'a, ana sa ran za a kwashe wani lokacimai tsawo, domin cimma matsaya tsakanin manyan jam'iyyun, wadanda suka kafa irin wannan gwamnati ta hadaka daga shekara ta 2005 zuwa 2009. Ranar Alhamis ta mako mai zuwa jam'iyya mai mulkin kasar ta Jamus CDU za ta gudanar da tattaunawa da jam'iyya mai muradun kare muhalli ta Greens, wadda ta samu kashi 8 cikin 100 yayin zaben da ya gabata.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Zainab Mohammed Abubakar