Kasashen duniya na kokarin sassanta rikicin Venezuela
February 8, 2019A ranar Alhamis ne dai aka yi taron da ke zama na tuntuba tsakanin kasa wanda kuma ya samu goyon bayan kungiyar tarayyar Turai. Jakadu na kasashen Latin Amirka 13 da wakilan kungiyar EU sun halarci taron. Bayan kwashe sa'oi hudu ana muhawara ba tare da sa ido na 'yan jarida ba shugabar sashin kula da harkokin kasashen waje na EU Federica Mogherini da Shugaban kasar Yurugai Tabare Vazquez sun yi taron manema labarai inda suka ce zaman tattaunawar da suka yi, ya yi amfani kasancewar sun cimma matsaya ta ganin an warware rikicin siyasar Venezuela cikin lumana. Haka zalika a cewar Mogherini, za su kuma ba da tallafi: Ta ce: ''har ila yau tattaunawar da aka yi ta nunar da cewa an fahimci miliyoyin al'umma na cikin hali na kaka na ka yi don haka kasashen sun amince da hada hannu wuri guda a ba da tallafi. Za a kuma a yi aikin tallafi bisa jagoraci na hukumar kula da 'yan gudun hijira ta MDD karkashin jagoranci na Edwardo Stein."