1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

An mayar da hakorin dan fafutikar neman 'yancin Kwango

Abdoulaye Mamane Amadou
June 20, 2022

Tun bayan kisan fitaccen dan fafutikar 'yancin kan Jamhuriyar Dimukuradiyar Kwango Patrice Lumumba, a karon farko an mika wa iyalinsa hakorinsa da aka cire.

https://p.dw.com/p/4Cx9n
Belgien DRK Alexander De Croo Jean-Michel Sama Lukonde
Hoto: OLIVIER MATTHYS/AFP/Getty Images

Kasar Bejiyam ta sake rokon al'ummar Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango afuwa, game da kisan fitaccen dan fafutikar neman 'yancin kasar Patrice Emery Lumumba, wanda turawan Bejiyam 'yan mulkin mallaka suka hallaka a birnin Katanga na kasar Kwango a shekarar 1961.

A gaban dan-dazon iyalan Lumumba a yayin wani bikin mika haurensa da 'yan mulkin mallakar Bejiyam suka cire bayan sun masa kisan gilla, Firaministan Bejiyam Alexander De Croo ya ce Bejiyam na cigaba da juyayin yadda aka kashe fitanccen dan fafutikar neman 'yancin, bayan da ta dauki alhakin kisan.